Thursday 30 October 2025 - 08:24
Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga hangen Limamim Juma’a na Bombay

Hauza/ Hujjatul islami walmuslimin Sayyid Ahmad Ali Abidi, wakilin Ayatollah al-Uzma Sistani a ƙasar Indiya kuma Limamin Juma’a na Bombay, ya bayyana cewa Iran a yau tana da matsayi mai girma a fagen ƙasa da ƙasa, tare da kiran da ya yi na yaƙi da mamayar kafafen yada labarai na maƙiyi, ƙarfafa ilimin hauza da kuma ƙulla alaƙa mai ƙarfi tsakanin ɗaliban addini da al’umma

Labaran Hauza - Yayin ziyararsa zuwa Iran, Hujjatul islami walmuslimin Sayyid Abidi ya kai ziyara ga Hauza News Agency inda ya yi hira da su. A cikin tattaunawar, ya jaddada muhimmancin ƙarfafa kafafen yaɗa labarai na hauza, karya takunkumin labarai na maƙiyi, haɓaka tsarin koyarwa a hauzohi, kare akidun addini, da faɗaɗa hulɗar ɗaliban addini da jama’a. Ya kuma bayyana ra’ayoyinsa game da ƙalubalen da hauzohi ke fuskanta a Indiya.

Wakilin Ayatollah al-Uzma Sistani a Indiya ya ce: "Iran ƙasa ce wacce ba kawai tana da ƙarfin siyasa da tsarin gwamnati mai ƙarfi ba, har ma tana da tushen ruhi mai zurfi. Wannan goyon baya yana fitowa ne daga Imamuz-Zaman, Hujjat ibn al-Hasan (Aj) wanda koyaushe ke kiyaye al’umma da ƙasarta. Imam ɗin kansa ya ce: idan ba saboda jagoranci da kulawarsa ba, da maƙiya sun hallaka mu."

Ya ƙara da cewa: "Wannan goyon bayan na musamman ni’ima ce da babu wata ƙasa a duniya da take da ita, kuma ba za a iya kalubalance ta ba. Nasarar Iran sakamakon haɗin gwiwar shugabanci mai hikima, addu’o’in mutane, goyon bayan masoyan Ahlul Baiti (a.s.), da basira da niyyar gaskiya ta al’umma ce. Haka kuma, tarukan addu’a a duk faɗin duniya sun taka muhimmiyar rawa wajen wannan nasara. Dukkan wannan ya samo asali ne daga tsarkin niyya da ƙaunar gaskiya, ba daga son kai ko son riba ba."

Limamin Juma’ar na Bombay ya jaddada cewa: "Ya kamata mu tuna cewa maƙiyi ba zai taɓa daina adawa ba. Duk lokacin da ya sha kaye, sai ya zama mafi hatsari; saboda haka, a ko da yaushe wajibi ne mu kasance cikin faɗakarwa da taka-tsantsan."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha